Labarai
Gwamnan jihar Kano Ya ce za’a ɗauki nauyin karatun tubabbun ƴan daba
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce yayi alfahari Da farinckin kasancewar sa a wannan taror Da Zai Dora Jihar Kano a sahun gaba Na kasancewar ta Jaha mafi karancin aikata laifuffuka a Nigeria
Haka zalika gwamnan Abba ya ce wannan taro ai kara tabbatar da taken kano ne na cibiyar kasuwanci da Ci gaban tattalin arziki
Dan haka abokan huldar Jiharmu ta Kano kamar ƴan kasuwa da masu masana’antu dake da buƙatar zuba jari da yin kasuwanci da kada su ji fargaba ta barazanar rashin tsaron dukiyarsu da lafiyarsu, Domin a yanzu Kano a karkashin wannan gwamnati ta samu tsaro na dundundun in shaAllahu
Dan haka wadannan matasa da suka yi abin da Allah Yake so na tuba da daina aikata manyan laifuffuka da kuma komawa cikin al’umma domin cigaba da rayuwarsu kamar yadda tsarin zamantakewa da mutuntakar al’ummarmu ya kunsa
Yafe musu da aka yi ba yana nufin sunci bulus bane, wannan yana nuna yafiya lokacin da mutum yayi nadama na da matukar muhimmanci wajen wanzuwar zaman lafiya cigaban Jiha da ma tattalin arzikin ta
Kano a yau ta kafa tarihin kasancewar Jiha ta farko da aka fara amfani da masalaha wajen dakile aikata laifuffuka da hana su baki daya
Ina farin cikin karbar wadannan matasa 222 da suka yi wa wannan gwamnati mubaya’a suka kauracewa aikata laifuffuka suka kuma yi alkawarin kasancewa mutane na gari, masu bin doka da oda da taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya
Kuma na sanar da al’umma cewar wadannan matasa sun sami horo na musamman daga masana a fannonin rayuwa daban-daban
Kuma muna da yaƙinin cewar wadannan matasa a shirye suke su shiga cikin al’umma domin ci gaba da rayuwarsu
Cikin bukukuwan da muka shiryawa wadannan matasa dan tabbatar musu su ma mutane ne har da gasar wasan kwallon kafa da aka gudanar inda ta fito da hazakar wasu daga cikin wadannansu
Daga karshe ina godewa ga dukkannin wadanda suka taimaka aka yi taro lafiya aka gama lafiya
You must be logged in to post a comment Login