Labarai
Gwamnan Kano Abba Gida-Gida ya ƙaddamar da rabon kayan karatu ga ɗaliban firamare da sakandare
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da rabon kayan karatu ga ɗaliban firamare da sakandare domin ƙara bunƙasa harkar koyo da koyarwa a makarantu na mataki na farko, inda ya ce wannan rabon kayan zai tallafa wajen samarwa da ɗalibai a mataki na farko ingantaccen ilimi
Gwamna Abba Kabir Yusuf yayi wannan jawabin ne a yau a ɗakin taro na Coronation dake fadar gwamnatin Kano yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan karatun ga dalibai
Gwamnan ya kuma ce ganin yadda daliban na Firamare da sakandare suke karatu cikin rashin ingantattun kayan karatu yasa gwamnati taga dacewar samar musu da kayan karatu
Gwamna Yusuf ya kuma ce ya baɗa wa’adin makwanni biyu a tattance ma’aikatan hucin gadi wato ƴan BEZDA domin a kawo masa sakamako domin aga ta yaya za’a samar musu da aiki na dindindin
Haka kuma yace la’akari da yadda ma’aikatan na BESDA suka shafe shekaru suna aiki ba tare da ai basu aiki ba da kuma ƙin biyan su hakkin su yaga dacewar basu aiki a wannan lokaci
Gwamna Abba ya kuma ce suma masu buƙata ta musamman ana sane da su domin suma akwai tsari na musamman da gwamnati tayi musu wajen samar musu da aikin yi da tallafa musu wajen yin karatu
Gwamnatin Kano ta samar da littattafan rubutu da na Kimiya sama da miliyan 2 da kuma kayan karatun masu buƙata ta musamman.
You must be logged in to post a comment Login