Labaran Kano
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kudi na shekarar 2024 sama da 357 billiyan
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kiyasin kasafin kudi sama da Naira biliyan 357 na kasafin kudin shekarar 2024 ga majalisar dokokin jihar
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan a yau Juma’a, ya ce daga cikin jimillar kasafin kudi na Naira biliyan 350, an ware Naira biliyan 215 domin gudanar da manyan ayyuka, yayin da kuma an amince da Naira biliyan 134 na kudaden da ake kashewa akai-akai
Gwamnan ya kara da cewa, bunkasa jarin dan Adam, inganta jin dadin al’ummar Kano, tabbatar da tsaron rayuka, samar da kiwon lafiya dabaru, samar da wadataccen abinci, samar da damammaki na samar da ayyukan yi, da karfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu, sune manyan ka’idojin gwamnatinsa
Gwamnan ya yabawa Majalisar Dokoki ta Jiha da ta taimaka masa a cikin ‘yan kwanakin da ya rike Jihar, wasu nasarorin da ya samu a cikin watanni 5 da suka wuce wanda ya sa Jama’a su yi farin ciki a cikin Birnin Ya ba da fifiko kan ilimi da suka hada da. daukar nauyin sake dawo da tallafin karatu na kasashen waje
You must be logged in to post a comment Login