Labarai
Gwamnan Kano Abba ya yi ganawar sirri da Kwankwaso

Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gudanar da wata ganawar sirri da jagoran NNPP kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, a gidansa da ke Miller Road.
Jaridar Daily Najeriya ta ruwaito cewa ganawar ta gudana ne cikin dare, inda gwamnan ya je gidan Kwankwaso tare da wani mutum mai shiga tsakani, domin tattauna muhimman batutuwan siyasa.
Bayan ganawar gwamna Abba Kabir Yusuf ya tashi zuwa kasar Faransa, inda ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Majiyoyi sun ce ganawar na da nasaba da yunkurin shawo kan Kwankwaso kan batun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki kasa.
You must be logged in to post a comment Login