Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tarihin Abba Kabir Yusuf da ya lashe zaben gwamnan Kano

Published

on

An haifi Abba Kabir Yusuf, a ranar 5 ga watan Janairun shekarar 1963 a karamar hukumar Gaya ta jihar Kano.

Abba Kabir Yusuf ya halarci makarantar Firamare ta Sumaila da ke karamar hukumar Sumaila a jihar ta Kano, kana daga bisani ya ta fi babbar sakandaren Lautai da ke karamar hukumar Gumel ta tsohuwar jihar Kano, inda ya kammala ta a shekarar 1980.

Ya shiga Kwalejin Fasaha ta tayayya da ke karamar hukumar Mubi a jihar Adamawa, inda ya samu shaidar karamar Diploma a fannin Fasahar gine-gine a shekarar 1985.

Abba Kabir Yusuf ya kuma tafi Kwalejin Fasaha ta Jihar Kaduna, domin samun shaidar kammala karatun babbar Diploma, a fannin Fasahar ma’adanan ruwa da kula da muhalli, a shekarar 1989.

Haka kuma ya yi hidimar kasa daga shekarar 1989 zuwa 1990 a ma’aikatar kare muhalli ta jihar Kaduna.

Bugu da kari, Abba Kabir yana da digiri na biyu a fannin dabarun kasuwanci da mulki.

Ya rike mukamin mai taimakawa tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, daga shekarar 1999 zuwa 2003.

Sa’annan ya rike mukamin kwamishinan ayyuka da gidaje da kuma sufuri a mulkin Kwankwaso na biyu, daga shekarar 2011 zuwa 2015.

Haka zalika ya yi takarar gwamnan Kano karkashin jam’iyyar PDP a shekarar 2019.

Allah ya albarkaci Abba Kabir Yusuf da ‘ya’ya gud 15 da kuma mata biyu.

 

Rahoton: Muhammad Sani Uba

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!