Labarai
Gwamnan Kano ya bayar da tallafin kuɗi ga masu sana’a akan madakatar tituna su 465
A wani yunkuri na inganta masu ƙananan kasuwanci, Gwamna Abba Kabir Yusuf a ya baiwa masu gudanar sana’o’i akan tituna tallafin kuɗi da adadinsu ya kai 465 da naira dubu hamsin kowannen su da aka zabo daga madakatu tara dake kan titunan birnin Kano.
Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya rabawa manema labarai.
Da yake gabatar da nasa jawabin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce an ba da wannan tallafi ne a bisa fifikon da gwamnatinsa ta ba wa marasa galihu musamman matasa da mata ta hanyar inganta sana’o’in su.
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi karin haske da cewa, a kwanakin baya gwamnatin jihar Kano ta baiwa mata 5200 tallafin kudi naira dubu 50,000 kowannensu kwatankwacin miliyan 26, kuma shirin ya fara samun sakamako mai kyau saboda yanayin zamantakewa da tattalin arziki na wadanda suka amfana.
Ya bukace su da su yi amfani da kudaden da aka ba su wajen faɗaɗa kasuwancin su ta yadda zai samar da tsari mai kyau na haɓaka tattalin arzikin jihar.
You must be logged in to post a comment Login