Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu koma amfani da Drone wajen dakile ta’addance- IGP

Published

on

Rundunar ‘yan sandan kasar nan, ta ce, ta na gab da kaddamar da kyamarorin tsaro na Drone domin magance matsalolin ta’addanci a fadin Najeriya.

Babban Sufeton ‘yan sanda na kasa Kayode Egbetokun, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke gabatar da mukala a jami’ar Ibadan da yammacn Litinin din makon nan.

Ya ce, duk da cewa, rundunar na da irin wadannan kyamarori, amma nan ba da jimawa ba rundunar za ta mayar da hankali kacokan kan amfani da na’urorin na Drone domin sanya ido a ko ina daga babbar shalkwatarta da ke birnin tarayya Abuja.

Babban Sufeton ‘yan sandan, ya kara da cewa, yin amfani da wannan tsari zai taimaka musu wajen hango bata gari duk lokacin da suke aikata laifuka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!