Connect with us

Labaran Kano

Gwamnan Kano ya nemi tallafin gwamnatin tarayya kan gobarar kasuwanni

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta samar da kayan aikin kashe gobara na zamani ciki har da tallafin jirgin sama, bayan sake barkewar gobara karo na biyu a Kasuwar Singer da ke cikin birnin Kano.

 

Gwamnan ya yi wannan kira ne a lokacin da ya isa sashen Gidan Gilas na kasuwar yayin da gobarar ke ci gaba da tashi, inda ta lalata shaguna da dukiyoyi masu yawa. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.

 

A cewar sanarwar, gwamnan ya jaddada cewa samar da kayan aikin kashe gobara na zamani da sauran muhimman kayayyaki zai taimaka wajen dakile irin wannan ibtila’i da kuma kara karfin hukumomin kashe gobara wajen tunkarar lamarin gaggawa, musamman a manyan cibiyoyin kasuwanci a fadin kasar nan.

 

Ya kuma yaba da kokarin jami’an kashe gobara na jihar da sauran hukumomin tsaro bisa jajircewarsu wajen shawo kan gobarar. Haka zalika, ya bukaci ‘yan kasuwa da mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an agaji hadin kai domin dakile gobarar da kuma kare rayuka da dukiyoyi.

 

Kasuwar Singer na daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a Kano, kuma wannan ne karo na biyu da gobara ta tashi a kasuwar cikin shekarar 2026

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!