Connect with us

Labaran Kano

Gwamnan Kano ya tsige shugaban ma’aikatan jihar

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sauke Shugaban Ma’aikatan Jiha, Alhaji Abdullahi Musa, daga mukaminsa.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yammacin yau Talata.

 

Sanarwar ta ce matakin na daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na sake fasalta aikin gwamnati domin kara inganta shi, da kuma kyautata yadda hukumomin gwamnati ke gudanar da ayyukansu.

 

Gwamnan ya gode wa tsohon Shugaban Ma’aikatan bisa gudunmawar da ya bayar da kuma jajircewarsa wajen yi wa Jihar Kano hidima a lokacin da yake kan mukamin.

 

Ya kuma yi masa fatan alheri da nasara a rayuwarsa ta gaba.

 

Sanarwar ta kara da cewa gwamnan ya umurci Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, wadda ke matsayin Babbar Sakatare mai kula da sashen Admin and General Services a Ofishin Majalisar Zartarwa, ta rike mukamin Shugabar Ma’aikatan Jiha na rikon kwarya, har sai an nada sabon mai mukamin na dindindin.

 

Haka kuma an umurci tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar da ya mika ragamar ofishin ga mai rikon mukamin nan da ranar Laraba 11 ga Maris, 2026.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!