Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnan Nasarawa ya kaddamar da ma’aikatar kula da harkokin kan iyakoki

Published

on

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya kaddamar da ma’aikatar kula da kan iyakoki na jihar tare da manbobin da za su yi aiki a hukumar.

Gwamnan Abdullahi Sule a ya yin kaddamarwa ya nada shugaban majalisar gudanarwa na kwalejin ilimi na jihar dake Akwanga.

Gwamnan dai ya kaddamar da hukumar ne tare da shugaban gudanarwa na kwalejin ilimi na jihar  a babban dakin taro na Aliyu Akwe Doma dake fadar gwamnatin jihar.

Har ila yau, gwamnan ya bayyana cewar, kaddamar da hukumar ya zama wajibi don warware matsalolin kan iyakoki da jihar Nasarawa da makwabtan ta kew fuskanta da kuma kan iyakokin kananan hukumomi na jihar.

Abdullahi Sule ya ce ma’aikatar kula da harkokin  kan iyakokin zai taimaka wa jihar  wajen warware rikicin kan iyakoki na cikin gida da kuma tabbatar da ana bin dokokin da aka shinfida na layunka da aka gindaya.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!