Labarai
Gwamnan Zamfara ya bukaci Musulmi su dage da addu’o’in neman zaman lafiya

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Dare, ya bukaci musulmi da su dage da addu’o’in neman zaman lafiya a jihar da ma Najeriya baki daya yayin bukukuwan Sallah.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya fitar.
Sanarwar ta nuna cewa gwamnan ya taya musulmi murnar kammala azumin Ramadan, tare da bayyana sallah a matsayin lokaci na godiya, hadin kai da sabinta kyawawan dabi’u.
You must be logged in to post a comment Login