Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Gwamnati bata shirya gyara harkar Almajirci a Kano ba – Alhaji Inuwa

Published

on

Cibiyar da ke nazari kan rayuwar almajirai mai suna 2030 ta zargi gwamnatin Kano kan rashin samar da inganta harkar almajirci a jihar.

A cewar cibiyar harkar almajirci ta sauya salo a yanzu, sakamakon yadda ake ganin shigowar sabbin abubuwan da babu su a harkar almajirci a baya.

Shugaban cibiyar a nan kano Alhaji Inuwa Ahmad ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na nan tashar Freedom radio da shirin ya mayar da hankali kan yadda a ke samun yawaitar almajirai a yanzu.

Alhaji Inuwa Ahmad yace, har yanzu gwamnatai bata shirya gyara bangaren ba.

“Da alama har yanzu gwamnati bata shirya kakkabe harkar almajirci a kasar nan ba, ko kuma fito da ingantattun tsari da za su kyautata harkar anan Kano”.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!