Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Bidiyo

Faifan bidiyon dala: Ba harka ta bace, ba ruwa na – Shugaban majalisar dokokin Kano.

Published

on

Shugaban majalisar dokokin jihar Kano Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya ce, batun bincike ko kalaman da gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi abaya-bayan kan faifan bidiyon dala wanda a shekarun baya aka yi zargin an ganshi yana karbar na goro a wajen ‘yan kwangila bai shafeshi ba.

A cewar Hamisu Ibrahim Chidari shi bashi da ta cewa kan wannan al’amari.

Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin ‘barka da hantsi’ na tashar freedom radio da ya gudana a ranar laraba.

Da aka tambaye shi cewa, a waccan lokaci majalisa ta ce za ta gudanar da bincike kan wannan batu, shin menene sakamakon binciken?

Sai ya ce ” to ai bibiya ya kamata ku yi a can aga meye karshen labarin, amma ni ba harka ta bace saboda haka bazan ce komai ba kan wannan al’amari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!