Labarai
Gwamnatin Kano zata kashe fiye da Biliyan 11 wajen magance zaizayar kasa

Gwamnati jihar Kano zata kashe fiye da biliyan Goma sha daya wajen magance zaizayar kasa da samar da titi a yankin Gayawa, Bulbula da wasu gurare cikin karamar hukumar Ungoggo.
Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusif, ne ya bayyana hakan lokacin da yake mika diyar kudi ga mutanen da aikin ya shafi gidajensu.
Gwamnan ya kara da cewa Gwamnati zata tabbatar da biyan duk Wanda aikin ya shafa diyya kafin farawa inda za a fara da raba miliyan dari shida ga wasu cikin mutane da aikin zai shafa dan samun sabon matsuguni.
Ya kuma kara da cewar Gwamnatin sa zata ci gaba da bibiyar duk inda zaizayar kasa take a fadin jihar Kano dan daukar matakin da ya kamata.
Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya ce aikin zai shafi gidaje fiye da dari biyu kuma Gwamnati tayi kyakkyawan tsari wajen biyansu diyya.
You must be logged in to post a comment Login