Labarai
Gwamnati ta aike da kudirin sake bude hukumar yaki da cin – Malami
Gwamnatin tarayya ta aikewa majalisaar dokokin kasar nan kudirinta na sake bude sabuwar hukumar yaki da cin hanci da rasahawa a fadin kasar nan.
Ministan Shari’a kuma antoni Janar na Kasa Abubakar Malami mai mukamin SAN ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartas ta kasa da ya gudana a jiya.
Abubakar Malami ya ce da zarar majalisar ta amince da kudirin za’a samar da hukumar da zata dinga kula da ayyukan cin hanci da rashawa a fadin kasar nan baki daya.
Ministan ya ce kudirin sake bude sabuwar hukumar ta yaki da cin hanci da rashawa ya biyo bayan yanda ayyukan cin hanci da rashawa sukayi yawa a kasar nan.
A cewar sa Hukumar zata yi aiki da hukumomin tsaro a kasar nan da suka hadar da rundunar ‘yan’sanda da hukumar tsaron Sirri ta DSS Da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da takwararta ta ICPC.
You must be logged in to post a comment Login