Connect with us

Labarai

Rundunar soja ta samu nasarar lalata maboyar ‘yan ta’adda a Zamfara

Published

on

Rundunar sojin kasar ta ce dakarun ta na Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan tada kayar baya da ke boye a kauyen Kwiambana a jihar Zamfara tare da lalata maboyar ta su.

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin kasar nan Major janar John Enenche ya fitar a jiya Laraba.
John Enenche ta cikin sanarwar ya bayyana cewa dakarun sunyi nasarar kashe ‘yan bindigar da ke boye a kauyen inda nan take suka lalata maboyar ta su.

Sanarwar ta kuma ce ko a ranar 15 ga watan da muke ciki sai da dakarun Operation Wutar Daji suka yi nasarar fatattakar ‘yan tada kayar baya a Arewa maso bagashin kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!