Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnati ta amince a riƙa ajiye abin hawa da Lodi a filin Idi

Published

on

Shugaban kasuwar Kantin Kwari a Kano ya ce gwamnati ta amincewa ƴan kasuwa su riƙa ajiye abin hawa da Lodi a filin Idi da ke Ƙofar Mata Don rage cinkoso a kasuwar.

Shugaban kasuwar Alhaji Hamisu Sa’adu Dogon Nama ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a wani ɓangare na samar da tsari ga kasuwar.

Alhaji Hamisu Sa’adu Dogon Nama ya kuma ƙara da cewa rashin cushewar kasuwar shi zai taimaka wajen samar da tsari a cikin ta.

Wakilinmu Umar Abdullahi Sheka rawaito cewa shugabancin kasuwar ya ce, zai dau mataki ga duk wani ɗan kasuwa da aka samu da karya dokar kasuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!