Labarai
Akwai bukatar samar da kasuwar mata zalla a Kano
Shugabar taron baje kolin sana’oin da mata ke gudanarwa Hajiya Fatima Ali Hamisu ta bayyana cewa akwai bukatar a samar da kasuwar da mata zalla zasu rinka gudanar da siye da siyarwa domin rage cakuduwa tsakanin maza da mata a kasuwanni.
Hajiya Fatima Ali Hamisu ta bayyana hakan yayin taron wayar da kan mata kan yadda za su sayar da kayayyakinsu wanda ya gudana a nan jihar Kano.
Ta ce samar da irin wannan kasuwa zai yi dai-dai da tsarin da jihar Kano ke kai na shari’ar Musulunci tare da tsaftace kasuwanci.
LABARAI MASU ALAKA
Har yanzu mata na fuskantar cin zarafi- Barrista Hussaina Aliyu
Mata basu fiya karbar rashawa ba -Muhuyi Magaji Rimin Gado
Wasu daga cikin matan da suka gudanar da bajakolin kayayyakin su a kasuwar sun bayyana jin dadin su musamman yadda mata suke shigowa dan gudanar da sayyar su ba tare da maza ba, tare da yabawa da wannan sabon tsari.
Da yawa daga cikin matan da suka ziyarci bajakolin dan gudanar da siyayyar kayayyaki sun yi kira ga gwamnati da ta samar musu da kasuwa ta mata zalla da zasu dinga zuwa dan siyayya ba tare da suna chakuduwa maza da mata ba.
You must be logged in to post a comment Login