Labarai
Gwamnati ta samar da mafita wajen dogaro da kai na kasa-Dr Bello Ado
Masanin tattalin arziki dake jami’ar Bayero Dr Bello Ado ya ce bullar cutar Corona ta shafi tattalin arzikin kasar nan, duba da yadda hada-hadar kasuwanci ta ragu baya da koma baya da shigo da kayayyaki daga kasar China ya haifar.
Dr. Bello Ado, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin barkada Hantsi da ya yi duba kan yadda bullar Cutar Corona ta shafi tattalin arzikin kasar nan da sauran bangarori.
Masanin ya kara da cewa ya zama wajibi Najeriya ta dauki matakin magance wannan matsala don kuwa matukar aka ci gaba da dogara da kasashen ketare, wajen tafiyar da harkokin kasuwanci a kasar nan akwai yiwuwar wata rana kasar ta tsaya cik.
Labarai masu alaka.
Coronavirus: Shaguna sun fara daukar matakai a Kano
Covid-19: Masana a Kano sun yi tsokaci kan Coronavirus
Da yake nasa, tsokacin shugaban kungiyar masu hada maguguna ta kasa reshen jihar Kano, Alhaji Bala Mai Kudi, yace har yanzu ba’a samu maganin da ke warkar da cutar ba ta Corona in da ya shawarci al’umma da su dau matakan da ya kamata don kare kan su daga kamuwa da cutar.
Bakin sun yi kira ga gwamnati da ta samar da hanyoyin rage dogaro da kayayyakin kasashen ketare, kasancewar dogaro da kasashen waje shi ne ke kawo tarnaki ga tattalin arzikin kasar nan da zarar an samu wani tasgaro.
You must be logged in to post a comment Login