Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Buhari ya yi ganawa ta Internet kan rikicin Mali da kungiyar ECOWAS

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci zaman da shugabannin kungiyar bunkasa tattalin yammacin Afrika ECOWAS ke yi don lalubo hanyoyin sasanta rikicin kasar Mali.

Shugaba Buhari ya halarci zaman na yau ta kafar Internet a fadar sa da ke Villa a Abuja.

A yayin zaman na yau, wanda shugaban kungiyar kuma shugaban kasar Jamhuriyar Niger Mahmadou Issoufu ke jagoranta.

Wannan dai shi ne karo na biyu da kungiyar ta yi zama tun bayan da sojoji suka hambarar da zababban shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita.

Tun da fari dai, Sojojin da suka karbe mulki sun bayyanawa jakadan ECOWAS a kasar mali kuma tsohon shugaban kasar nan Goodluck Jonathan da sauran wakilan kungiyar ta ECOWAS cewa suna bukatar shekrau uku kafin  mika mulki ga hannun zababbiyar gwamnati.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!