Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnati zata sayo wa Abduljabbar Sahihul Bukhari da Muslim

Published

on

Gwamnatin Kano za ta saya wa Malami Abduljabbar Kabara litattafan Sahihul Bukhari da Muslim.

Yayin zaman shari’ar na yau a babbar kotun shari’ar Musulunci mai lamba ɗaya da ke Ƙofar Kudu lauyan masu ƙara Mamman Lawan Yusufari SAN ya roƙi kotu ta amince da buƙatar malamin na a bashi dama ya yiwa shaidu tambayoyi.

Kotun ta amince, bayan da yayi nisa da tambayoyin ne sai ya ɗauko wani littafi ya ci gaba da tambayoyi, hakan ya sanya lauyan masu ƙara ya yi suka.

Ya ce, ya kamata a san wane littafi yake kawo wa, nan take malamin ya ce, litattafai biyu ne a haɗe matani da sharhi.

Hakan ya sa mai gabatar da ƙara ya roƙi kotu da ta bada dama a kawo litattafan Bukhari da Muslim, kuma matani ba sharhi ba.

Sai dai ko da aka waiwayi malamin ya ce, yana buƙatar a bashi litattafan ya duba kafin dawowa kotu, amma mai shari’a bai amince ba, inda ya ce sai dai malamin ya sayi nasa.

A nan ne Malam Abduljabbar ya ce, ba shi da kuɗi saboda tunda aka tsare shi baya sayar da komai.

Jin hakan ne sai lauyoyin Gwamnati suka ce, Gwamnati zata saya masa litattafan, nan take Malamin ya yi godiya.

Wakilinmu Aminu Abdu Baka Noma ya rawaito cewa kotu ta ɗage sauraron shari’ar har zuwa ranar 25 ga watan Nuwamban da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!