Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

An Tashi Lafiya

Gwamnatin Afghanistan ta haramta cakuɗuwar mata da maza a aji

Published

on

Gwamnatin Taliban a kasar afghanistan ta samar sa sabon tsarin karatu, wanda ya haramtawa mata yin karatu tare da maza, wanda hakan na nufin za’a raba ajujuwan maza daban na mata ma daban.

Hakan ya fito ne ta bakin Ministan Ilimi Abdulbaqi Haqqani , ya kuma tabbatar da cewa lalle za su bawa mata damar yin karatu amma ba tare da cudanya da maza ba.

Ministan ya kara da cewa, za kuma su tace irin darusan da ya dace ana koyarwa a makaratun.

Idan za’a iya tunawa dai, a zamanin mulkin na taliban na shekarar 1996 da kuma na shekarar 2001, sun haramtawa mata yin karatu a fadin kasar. Amma sai dai a wannan karan sun yi alkawarin cewa zasu bawa mata damar su yi karatu har ma da yin aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!