Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Borno za ta ginawa fulani Ruga don kiwon dabbobi

Published

on

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya amince da bayar da filin da za a gina Ruga a Jihar domin kiwon shanu da sauran dabbobi.

Babagana Zulum ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci ministan harkokin noma, Alhaji Sabo Nanono a ofishinsa da ke birnin tarayya Abuja, inda suka tattauna shirin gwamnatin tarayya a kan Ruga.

Ministan ya yabawa kokarin gwamnan har ma ya ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta marawa shirin baya har zuwa kammalawa.

A yayin ziyarar, gwamna Babagana Zulum yana tare da kwamishinan harkokin kiwo, Modu Walama da mashawarcinsa kan harkokin kiwo, Tijjani Gwani Modu da kuma babban jami’in shirin Ruga na Jihar, Musa Inuwa Kubo.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!