Labarai
Gwamnatin Ganduje ta bai wa Triumph shagunan fiye da Naira Biliyan 1 don samun kudin shiga
Gwamnatin jihar Kano, ta bai wa madaba’ar Triumph kimanin kaso Ashin da Biyar na shagunan sabuwar kasuwar canjin kudin kasashen ketare ta zamani domin madaba’ar ta dogara da kanta ta hanyar samun kudaden shiga.
Da take mika makullan shagunan ga Manajan Daraktan madaba’ar a yau Laraba, wakiliyar kamfanin da ya gina kasuwar Hadiza Abdulkadir, ta ce, tun a ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2020 ne gwamnatin jihar Kano da kamfanin suka sanya hannu kan yarjejeniyar zuba hannun jari ta hanyar gina shagunan.
Hadiza Abdulkadir, ta kara da cewa “Kason gwamnatin kano a rukunin shagunan ya kai na darajar Naira Biliyan daya miliyan dari hudu da dubu dari shida da ashirin da biyar”.
Haka kuma ta ce, “A dai cikin kunshin yarjejeniyar tsakanin gwamnatin Kano da kamfanin nasu, akwai gina wa madaba’ar ta Triumph sabon matsuguni a rukunin gidaje na Shiek Kariballah Nasiru Kabara da ke kan titin zuwa Zaria, kuma tuni an kammala sun koma ciki.”
A nasa bangaren, Manajan Daraktan madaba’ar ta Triumph Malam Lawal Sabo Ibrahim, cewa ya yi shagunan za su taimaka wa kamfanin wajen sayen karin kayan aikin da zai kara inganta ayyukansu tare da samar wa gwamnati kudaden shiga.
Haka kuma ya ce, “ kaso Ashirin da biyar din ya kama kimanin shaguna Sittin da Hudu cikin dari na adadin dukkan shagunan da aka gina a wurin.”
Manajan Daraktan na kamfanin Triumph Malam Lawal Sabo Ibrahim,
ya kuma yaba wa gwamnatin jihar Kano bisa bada shagunan yana mai cewa za su kula da su yadda ya dace.
You must be logged in to post a comment Login