Kiwon Lafiya
Gwamnatin Jigawa ta rage wa ma’aikata lokacin aiki
Gwamnatin jihar Jigawa ta rage wa ma’aikatan jihar lokacin aiki na awanni 2 a yayin watan azumin Ramadana mai girma na wannan shekara ta 2019.
Mai Magana da yawun ofishin shugaban ma’aikata na jihar ta Jigawa Alhaji Isma’il Ibrahim ya bayyana hakan a birnin Dutse a jiya Talata 7 ga watan Mayu ta cikin wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema labarai.
A cewar Alhaji Isma’ila Ibrahim a halin yanzu ma’aikatan jihar za su je wuraren aiki ne da misalin karfe 9 na safiya su kuma tashi da misalin karfe 3 na yamma a tsakanin ranakun Litinin zuwa Alhamis maimakon su je wuraren ayyukan su da misalign karfe 8 su kuma tashi karfe 5 na yamma.
Mai Magana da yawun ofishin shugaban ma’aikatan ya kuma yi bayanin cewar, makasudun daukar wannan mataki shi ne, domin baiwa ma’aikatan jihar damar bautawa Allah a yayin azumi da kuma yin bude baki akan lokaci.