Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin Jigawa ta rage wa ma’aikata lokacin aiki

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta rage wa ma’aikatan jihar lokacin aiki na awanni 2 a yayin watan azumin Ramadana mai girma na wannan shekara ta 2019.

Mai Magana da yawun ofishin shugaban ma’aikata na  jihar ta Jigawa Alhaji Isma’il Ibrahim  ya bayyana hakan a birnin Dutse a jiya Talata 7 ga watan Mayu ta cikin wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema labarai.

A cewar Alhaji Isma’ila Ibrahim a halin yanzu ma’aikatan jihar za su je wuraren aiki ne da misalin karfe 9 na safiya su kuma tashi da misalin karfe 3 na yamma a tsakanin ranakun Litinin zuwa Alhamis maimakon su je wuraren ayyukan su da misalign karfe 8 su kuma tashi karfe 5 na yamma.

Mai Magana da yawun ofishin shugaban ma’aikatan ya kuma yi bayanin cewar, makasudun daukar wannan mataki shi ne, domin baiwa ma’aikatan jihar damar bautawa Allah a yayin azumi da kuma yin bude baki akan lokaci.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,434 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!