Labarai
Gwamnatin Kaduna ta gargadi makarantu masu zaman kansu su guji karin kudin makaranta

Gwamnatin jihar Kaduna ta gargadi makarantu masu zaman kansu a jihar da su guji yin karin kudin makaranta ba tare da sahalewar gwamnati ba.
Cikin wata sanarwa da babbar darakta mai kula da makarantu masu zaman kansu a ma’aikatar ilimin jihar, Mercy Bainta Kude ta fitar, ta ce gwamnati ba ta amince da yin karin kudin makaranta ba tare da saninta ba.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da aka koma zangon farko na sabuwar shekarar karatu ta 2025 zuwa 2026.
A cewar sanarwar bai kamata makarantun su kara kudin ba, a daidai lokacin da gwamnatin jihar ke shirin rage kudin makaranta.
You must be logged in to post a comment Login