Labarai
Gwamnatin jihar Kano zata inganta gidan zoo – Ranar yawon buɗe ido ta duniya
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta inganta gidan adana namun daji na jihar domin ƙara samun baƙi masu shigowa daga sassa daban-daban.
Kwamishinan ma’aikatar al’adu da yawon buɗe ido na jihar Alhaji Ibrahim Ahmad ƙaraye ne ya bayyana hakan, a wani ɓangare na bikin ranar yawon buɗe ido da ake gudanarwar kowacce shekara.
Ahmad ƙaraye ya ƙara da cewa tuni dokoki suka yi nisa wajan tabbatar da da gyara harkokin yawon buɗe ido da kuma al’adu.
“Zamu tabbatar da dokar hana shan shisha a wuraren shaƙatawa da kuma ƙananan yaran da suke zuwa hotel, sai kuma masu zuwa gidan biki da baƙin gilashin mota, tare da kaiwa dare a wajan bikin” in ji Kwamishinan.
Majalisar ɗinkin duniya ce ta ware ranar 27 ga watan satumbar kowacce shekara domin tunawa da irin muhimmancin da yawon buɗe ido ke dashi.
You must be logged in to post a comment Login