Labarai
Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudirinta na magance matsalar karancin gidaje

Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudirinta na magance matsalar karancin gidaje da ke addabar al’ummar jihar.
Kwamishinan gidaje da ci gaban birane na jihar Kano, Arc. Ibrahim Yakubu Adamu, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manyan jami’an ma’aikatar.
Arc Adamu ya bayyana cewa tun bayan samar da ma’aikatar, ta gano wuraren da za a aiwatar da aikin samar da gidaje karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, da suka hadar da garin Lambu cikin karamar hukumar Tofa, da Yargaya a karamar hukumar Dawakin Kudu,
Da kuma kammala ayyukan gidajen Kwankwasiyya da Amana da kuma Bandirawo.
Hakan yasa, kwamishinan ya shawarci manyan ma’aikatan ma’aikatar da su kasance masu tunani na aiki tare domin cimma muradun gwamnati na ci gaban jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login