Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin jihar Katsina ta bada umarnin bude makarantun mata biyar dake jihar

Published

on

Gwamnatin jihar katsina ta bada umarnin buden makarantun mata guda biyar da aka rufe sakamakon matsalolin tsaro a jihar.

Gwamnatin ta umarci makarantun da su yi gaggawar komawa daga gobe Laraba 24 ga watan maris na shekara 2021.

Gwamnati tace za’a bude makarantun kwanan ne domin ci gaba da karatun shekara ta 2020 da 2021 don karasa zangon karatu na farko.

Makarantun da lamari ya shafa sun hadar da sakandiren gwamnati ta Unit da ke Malumfashi da sakandiren SUNCAIS Katsina, sai sakandiren yan mata ta Dutsin Safe.

Sauran su ne: sakandiren yan mata ta Arabiyya da ke Dutsinma, sai sakandiren yan mata ta Deaf da ke Malunfashi da kuma sakandire ta masu lalurar gani da ke Katsina.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!