Connect with us

Manyan Labarai

Gwamnatin jihar Legas ta dakatar da bikin ranar yancin kai

Published

on

Gwamnatin jihar Lagos ta soke bikin ranar yancin kan Najeriya, sakamakon annobar Covid-19.

Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu wanda ya bayar da umarnin a wata sanarwa da ya fitar ya ce an soke bukukuwan da ake yi a irin wannan ranar ne da suka hadar da fareti domin kaucewa taruwar jama’a sama da hamsin.

Ya ce jihar ta zabi soke yi bikin murnar zagayowar ranar yancin kan ne saboda kaucewa yaduwar cutar COVID-19.

Gwamnan ya taya mazauna jihar murnar wannan rana inda ya shawarce su da su yi bikin cikin nutsuwa a gida tare da yi wa kasa addu’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!