Labarai
Gwamnatin jihar Taraba ta sanar da rufe makarantun kawana sakamakon satar dalibai

Gwamnatin jihar Taraba a Najeriya ta umarci dukkan makarantun sakandare, na gwamnati da masu zaman kansu na kwana da su gaggauta tura ɗalibai gida saboda ƙarin matsalar tsaro a fadin ƙasar nan.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishiniyar Ilimi ta Jihar, Dr. Augustina Godwin, ta fitar a madadin Gwamna Agbu Kefas.
Hakan dai ya biyo bayan yawaitar sace sacen-sacen dalibai da ya ke cigaba ta ta’azzara musamman a arewacin kasar.
You must be logged in to post a comment Login