An Tashi Lafiya
Gwamnatin Kaduna ta musanta jita-jitan da ke cewa zata dakatar da layukan sadarwa a Jihar
Gwamnatin jihar Kaduna, ta sanar da cewa bata da nufin dakatar da layukan sadarwa, kamar yadda ake ta yaɗa jita-jitan cewa zata aiwatar da hakan.
Hakan ya fito ne ta bakin babban mai baiwa gwamnan Kaduna shawara a harkar yaɗa labarai Muyiwa Adekeyi, ya kuma bayyanawa Freedom Radio cewa “Gwamnatin Kaduna ba ta da nufin dakile kafar sadarwa, haka kuma ba ta sanar da yin hakan ba”.
Ya kuma ce “bamu nemi gwamnatin tarayya da ta dakatar da layukan sadarwa ba, Muna fatan al’ummar garin Kaduna za su yi watsi da waccan jita-jita, tare da cigaba da aiwatar da al’amuran su na yau da kullum ba tare da fargaba ba.
A kwana-kwanan na ne dai wasu jihohin ƙasar nan suka ɗauki sabbin matakan tsaro, wanda har ya kai ga Gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da layukan sadarwa.
You must be logged in to post a comment Login