Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Tsaro

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar ta ɓaci Zangon Kataf

Published

on

Hukumomi a jihar Kaduna sun sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Unguwannin Juju da Mabuhu da Ungwar Wakili duk a yankin karamar hukumar Zangon kataf.

Sanya dokar dai ya biyo bayan gano gawarwaki 10 bayan da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai hari yankunan.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban karamar hukumar Zangon Kataf Yabo Ephraim ya fitar a yau Lahadi.

Sanarwar ta ce, sanya dokar na daga cikin matakan daƙile matsalolin tsaro da kuma baiwa sojojin damar dawo da zaman lafiya a yankin.

Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar ta Kaduna ba ta ce komai a kan lamari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!