Labarai
Gwamnatin Kaduna za ta daukaka kara kan hukuncin El Zazzaki
Gwamnatin jihar Kaduna ta kudiri aniyar daukaka kara kan hukuncin da babbar kotun tarayya dake jihar ta yanke na barin shugaban mabiya darikar shi’a Ibrahim El-zazzaki da mai dakin sa Zeenatu zuwa kasar India don neman magani.
Wanda ya shigar d akarar Mr Dari Bayero ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Kaduna, cewa duk da hukuncin da aka yanke a ranar Litinin wanda umarnin ya nemi da hukumar tsaro ta farin kaya DSS da ta bibiya da umarnin kuma wacce shugaban mabiya darikar ta Shi’a ke hannun su tun a shekara ta 2015, amma gwamnatin jihar take ganin yuwar ta daukaka karar.
Mr, Dari Bayero yakara da cewar, gwamnatin jihar ta Kaduna babu tantama zata daukaka kara kan hukuncin da babbar kotun jihar ta yanke kafin shugaban mabiya darikar ta shi’a ya tafi kasar India don duba lafiyar sa.
Mai karar a madadin gwamnatin jihar ta Kaduna ya ce dole a sake duba yarjejeniyar tafiyar da shugaban shi’ar zai da maid akin sa don duba lafiyar sa a kasar India.
Sai dai lauyan wanda ake kara Femi Falana ya ce bai ga dalilin da zai sanya a sake daukaka kara kan hukuncin da babbar kotun jihar t ayanke ba.