Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NAHCON: ta yi jigilar maniyatan aikin hajji dubu sittin da biyar a bana

Published

on

Kimanin ‘yan Najeriya maniyata aikin hajjin bana dubu sittin dabiyar ne hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON tayi jigilar su zuwa kasar mai tsariki.

 

Wani babban jami’I a hukumar ta NAHCON Dr, Aliyu Tanko ne ya shedawa manema labarai a birnin Makkah cewa tuni hukumar ta kammala shirye-shirye don saukakawa maniyata aikin hajji don sauke farali wanda za’a fara a ranar Asabar mai zuwa.

 

Dr, Aliyu ya ce  hukumar ta kammala jigilar  dukkannin ‘yan Najeriya zuwa kasa mai tsarki kuma tuni suka fara yin ziyara wurare masu daraja.

 

Haka zalika ya yabawa hukumomin kasar Saudiya saboda hadin kan da suke baiwa hukumar ta NAHCON wajen ganin ‘yan Najeriya sun sami sauki a yayin yin jifan shedan

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!