Connect with us

Labaran Kano

Tsohon mai horas da Kano Pillars ya rasu

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ta sanar da rasuwar tsohon dan wasanta kuma tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles, Kabiru Baleria.

Kabiru Baleria ya rasu a yammacin yau talata bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Kakakin kungiyar ta Kano Pillars Lurwanu Idris Malikawa ya tabbatarwa da Freedom Radiyo rasuwar cikin wata tattaunawa da ya yi da Wakilinmu Aminu Halilu Tudun Wada.

Kano Pillars ta lallasa Delta Force da ci 6-1

Kano Pillars ta samu nasara karon farko a kakar wasanni ta bana

Magoya bayan Kano Pillars na kira da a kori mai horar da ‘yan wasan kungiyar

Marigayi Kabiru Baleria, ya rike kungiyar ta Kano Pillars, a matsayin mai horar da ita na rikon kwarya a karshen shekarar 2018, bayan karewar kwantiragin mai horar da ita na yanzu Ibrahim Musa Jugunu.

Marigayin ya kuma rike kungiyar kwallon kafa ta kasa ta matasa ‘yan kasa da shekaru 20 wato flying Eagles.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!