Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Abdul’aziz Garba Gafasa ya sake zama shugaban majalisar dokokin jihar Kano

Published

on

Sabon shugaban majalisar dokokin jihar Kano Abdul’aziz Garba Gafasa, ya sha alwashin tafiya tare da kowa da kowa ba tare da nuna fifikon jam’iyya ba.

Abdul’aziz Garba Gafasa, ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai bayan kama rantsuwar kama aiki.

Abdul’aziz Garba Gafasa wanda kuma dan majalisa ne mai wakiltar karamar Hukumar Ajingi, ya samu nasarar zama sabon shugaban majalisar ne ba tare da hamayya ba.

A cewar sa, jihar Kano kamar sauraqn jihohin Najeriya tana fuskantar matsaloli da dama wanda ya kamata masu rike da mukaman siyasa su mai da hankali don magance su; don ya bukaci hadin kan kowa da kowa don bunkasa tattalin arzikin jihar ta Kano.

Tun farko dai dan majalisa mai wakiltar karamar Hukumar Dala kuma mamba a jam’iyyar PDP Lawan Hussiani ne ya gabatar da kudirin bukatar zaben Abdul’aziz Garba Gafasa a matsayin sabon shugaban majalisar dokokin ta Kano, wanda kuma ba tare da bata lokaci ba, takwaransa da ke wakiltar Doguwa Salisu Ibrahmi Muhammad ya goyi bayan hakan.

Bayan da ta tabbata cewa babu wani dan majalisar da ke da sha’awar kalubalantar Abdul’aziz Garba Gafasa, akawun majalisar Abdullahi Alfa ya sanar da shi a matsayin sabon shugaban majalisar, inda kuma ba tare da bata lokacin ba ya rantsar da shi.

Haka zalika Hamisu Ibrahim Chidari wanda ya kasance mataimakin shugaban majalisar a majalisar ta takwas, ya sake dawowa ba tare da hamayya ba.

Kafatanin mambobin majalisar arba’in, in banda Wakilin mutanen Bunkure Muhammed Uba Gurjiya wanda aka jinkirta rantsuwar sakamakon rashin tantance bayanan kadarorin da ya mallaka daga Hukumar CCB sauran sun karbi rantsuwar kama aiki.

Tsohon shugaban masu tsawatarwa na majalisar Abdul Labaran Madari shi aka zaba a matsayin sabon shugaban masu rinjaye, Kabiru Hassan dashi Wakilin mutanen Kiru mataimakin shugaban masu rinjaye, sai kuma Labaran Ayuba Durum mai wakiltar Kabo a matsayin shugaban masu tsawatarwa.

Sauran sune: Hayatu Daurawar Sallau wanda aka nada a matsayin shugaban masu tsawatarwa bangaren masu rinjaye yayin da Isyaku Ali Danja daga Gezawa aka nada a matsayin sabon shugaban masu rinjaye sai kuma Garba Shehu Fammar da ya zama bulaliyar majalisar bangaren marasa rinjaye.

 

 

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!