Labarai
Gwamnatin Kano na shirin sabunta alakar ta da kasar Turkiyya

Gwamnatin Kano za ta kara sabunta alakar ta da kasar Turkiyya, musamman a bangaren zuba hannun jari domin habaka tattalin arzikin jihar.
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka lokacin da sabon jakadan kasar Turkiyya a Najeriya Mehmet Poroy ya kai ziyarar aiki da gabatar da kai ga gwamnan jihar.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano Dakta Sulaiman Wali, ya ce ziyarar sabon jakadan ta zo a daidai lokacin da gwamnati take sauya fasali Kano ta fannin tattalin arziki, kawata birni da samar kyakkyawar makoma ga al’ummar jihar.
Dakta Sulaiman Wali ya ce daga cikin alkawuran da sabon jakadan kasar ta Turkiyya a Najeriya Mehmet Poroy ya yi, akwai dawo da zirga-zirgar jirgin saman kasar na Turkiyya a jihar Kano, habaka fannin noma, ilimi da tallafawa yunkurin gwamnatin Kano wajen bunƙasa ababen more rayuwar jihar.
A nasa jawabin, jakadan kasar Turkiyya a Najeriya Mehmet Poroy ya jaddada ƙudirin ƙasarsa na ƙara faɗaɗa alaƙar kasuwanci da haɗin gwiwa da jihar kano, yana mai cewa akwai manyan damammaki da za a iya amfani da su wajen haɓaka ci gaba mai ɗorewa.
Sabon jakadan na kasar Turkiyya ya jaddada cikakken hadin kai da goyon baya ga dukkan tsarukan ci gaba da gwamnatin Kano ta bijiro da su.
You must be logged in to post a comment Login