Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da feshin maganin ƙwari

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da feshin maganin ƙwari a makarantun sikandire a wani mataki na yaƙi da ƙananan cututtuka.

Kwamishinan muhalli Alhaji Nasiru Sule Garo ne ya ƙaddamar da feshin a kwalejin fasaha ta GTC a ƙaramar hukumar Ungogo.

Ya ce, an ƙaddamar da feshin ne domin yaƙi da ƙananan cututtuka musamman cutar zazzabin cizon sauro da yake damun alumma.

Nasiru Sule Garo ya ce, “bayan ƙaddamar da aikin, gwamnatin jihar Kano za ta tabbatar an yi feshin a dukkanin makarantun kwana da makarantun tsangaya da ke Kano, domin yaki da ƙananan cututtuka a makarantun sikandiren.”

“Mun zo wannan makaranta ne domin mu ƙaddamar da feshin maganin sauro da kula da Beraye, Micizai da sauran ƙwari da za su iya cutar da alumma, wannan feshi ya kamata a ce ana yinsa duk shekara, Amma mun ji ana samun lauje cikin naɗi, amma muna tabbatar muku a wannan gwamnatin ta injiniya Abba Kabir Yusuf za ta ɗore da kowanne aiki.”

Ya kuma bukaci haɗin kan masu ruwa da tsaki da su tabbatar da aikin feshin ya yi nasara.

A jawabinsa, kwamishinan ilimi na jihar Kano Umar Haruna Doguwa wanda shugaban makarantun sikandiren kimiya da fasaha na jihar Kano ya wakilta ya yabawa gwamnatin Kano bisa farfado da shirin a makarantun sikandiren jihar da ya dade bawa gudanarwa a cikin su.

Shugaban makarantun sikandiren wanda darakta a hukumar Alhaji Garba Ahmed ya wakilta ya tabbatar da cewa ma’aikatar ilimi da hukumar na ganin shirin ya samu nasara domin kula da lafiyar daliban hukumar.

A jawabinsa na godiya, shugaban makarantar sikandiren ta GTC Ungogo Malam Mikail Hussain ya ce feshin yazo dai-dai a lokacin da ake bukatar sa laakari da yadda daliban makarantar suki fama a cutar zazzabin cizon sauro a yan baya-bayan nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!