Labarai
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da kwamitin gano musababbin rashin zuwan wasu yaran Makaranta

Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da kwamati na musamman da zai gano dalilan da suka sanya wasu daga cikin yaran Kano ba sa zuwa makaranta.
Kwamishinan ma’aikatar Ilimi na jihar Dakta Ali Haruna Makoda ne ya kaddamar da kwamatin mai Mambobi 18.
Ya ce, kwamatin zai samar da wata hanya ta musamman da za a rika koyar da dalibai sana’o’in Dogaro da kai kamar yadda Daraktan sashin yada labarai na ma’aikatar Balarabe Abdullahi Kiru yai Karin haske akai.
Ta cikin wata sanarwa da Daraktan sashen yaɗa labarai na ma’aikatar Ilimi Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar ya ce, mai bai wa gwamnan Kano shawara kan bunkasa Ilimi Alhaji Haladu Muhammad ne zai jagoranci kwamatin wajen gudanar da binciken.
You must be logged in to post a comment Login