Labarai
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin zamanantar da tashoshin Mota a faɗin jihar
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na zamanantar da dukkanin wuraren ajiye motoci a faɗin jihar domin samun daidaito.
Mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin sufuri Alhaji Danladi Idris Ƙarfi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyara hukumar KAROTA.
Alhaji Danladi Idris Ƙarfi ya ce, gwamnati za ta samar da ababen more rayuwa da wuraren shaƙatawa a tashoshin motoci da nufin samar da walwala ga matafiya.
Haka kuma yunƙurin zai jawo hankalin masu zuba jari don ci gaban tattalin arziƙin jihar Kano da ke zama cibiyar kasuwanci a kasashen Afirka.
Ya kuma nuna damuwarsa game da yanayin muhallin wasu tashoshin motoci da ya gani, yana mai bayyana su a matsayin abin kunya.
Alhaji Danladi Idris Ƙarfi ya ci gaba da cewa, gwamnati ta kammala shirye-shiryen siyan jiragen ruwa a wasu manyan koguna, irinsa na farko a jihar.
A nasa jawabin, Manajan Daraktan KAROTA Injiniya Faisal Mahmoud Kabir ya yabawa yunƙurin Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kafa ofishin mai bashi shawara na musamman kan harkokin sufuri da sauran mataimaka a fannin sufuri.
Ya kuma bada tabbacin bayar da goyon baya da haɗin kai daga hukumarsa domin ciyar da jihar gaba, inda ya jaddada ƙudirin KAROTA na magance ƙalubale daban-daban a fannin.
Hakazalika, mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin sufuri, Alhaji Danladi Idris Karfi, ya jagoranci tawagar da ta kai ziyarar gani da ido a wasu tasoshin motocin dake jihar.
Cikin su kuwa har da tshar mota ta Na’ibawa, da ta Malam Kato, da Yan Kaba, da kofar Ruwa, da Milltara, da kuma wuraren ajiye motoci na Rijiyar Lemo.
Hakan na cikin wata sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar sufuri Ibrahim Adamu Kofar Nassarawa ya fitar a ranar Asabar.
You must be logged in to post a comment Login