Manyan Labarai
Gwamnatin Kano ta Amince da kashe sama da Billiyan 40 domin aikin Gadar Ɗan Agundi da Tal’udu da wasu Ayyuka.
Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da sakin N40,353,117,070 domin gudanar da ayyuka daban-daban a jihar a zaman ta na Litinin 6 ga watan Nuwamba 2023
Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Kwamishinan yaɗa labaran jihar Kano Baba Halilu Ɗan tiye ya fitar ya kuma rabawa manema labarai
Majalisar ta amince da bayar da Naira 15,974,357,203 ga ma’aikatar ayyuka da gidaje ta jihar Kano don aikin gina gadar ƙasa da ta sama a Dan Agundi yayin da aka ware N14,455,507,265 na ginin gadar sana ta Tal’udu
Majalisar ta amince da sakin Naira miliyan 3,360,084,380 ga ma’aikatar ayyuka da gidaje domin sake gina magudanan ruwa da aka rufe a Jakara-Kwarin Gogau, yayin da aka amince da N1,579,755,966 don gina Kofar Waika – Unguwar Dabai – Yan Kuje Western bypass a karamar hukumar Gwale
Hakazalika an amince da Naira 1,350,460,874 ga ma’aikatar ayyuka da gidaje domin gina hanyar Unguwa Uku Ƴan Awaki-Limawa a karamar hukumar Tarauni, yayin da aka amince da N820, 262,071 don kammala Kanye-Kabo- Dugabau road a karamar hukumar Kabo
Daga cikin kudaden da aka bawa ma’aikatar ayyuka da gidaje domin gudanar da ayyuka daban-daban sun hada da N802,695,617 don kammala hanyar Kofar Dawanau-Ɗandinshe-Kwanar Madugu, an kuma ware N458,443,067 domin sake bayar da kwangilar gina gadojin masu tsallaka titi a wurare daban-daban a fadin jihar, yayin da aka amince da Naira 420,000,000 don gyara fitilun manyan tituna
Majalisar ta kuma amince da sakin N200,537,271 ga ma’aikatar ayyuka da gidaje domin biyan kuɗaɗe da kwangilar gyaran hanyar Kwanar Kwankwaso da ke karamar hukumar Madobi, da kuma N107,658,975 na gyaran hanyar cibiyar ajiya da gyaran hali da koyar da sana’a dake Kiru
Majalisar zartaswa ta amince da sakin kuɗaɗe ga ma’aikatar lafiya ta jihar da suka kai N53,654,223 don siyan kayayyaki da magunguna da ake bukata don baiwa cibiyoyin kiwon lafiyar domin samar da taimakon Gaggawa ga Mata da Yara kyauta. Sai kuma N37,005,000 don samar da rigakafin cutar Diphtheria a cikin ƙananan hukumomi 22 na gaɗin jihar
Majalisar ta amince da kudi naira miliyan 56,763,475 ga ma’aikatar ilimi ta jiha domin sake gina wani ɓangare da ya ƙone a kwalejin koyon addinin musulunci da shari’a ta Aminu Kano
You must be logged in to post a comment Login