Labaran Kano
Gwamnatin Kano ta bayyana gamsuwar ta da zabukan cike gurbi da aka yi

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba da yadda aka gudanar da zaben cike gurbi a jihar ba tare da tashin hankali ko magudi ba.
Gwamnan Ya bayyana hakan ne bayan kammala zaben cike gurbi da hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC ta shirya a mazabun Kano Municipal da Ungogo na majalisar dokokin jihar.
Inda ya bayyana cewa yanzu zamanin tayar da hankali yayin kada kuri’a ya wuce, yana mai jaddada cewa zaben na wannan karon ya gudana ba tare da rikici ko amfani da makamai ba, haka kuma ba a samu wata alamar magudi a zaben ba.
Sannan ya yabawa jami’an tsaro da ma’aikatan INEC kan yadda suka gudanar da aikinsu, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen tabbatar da sahihin zabe.
You must be logged in to post a comment Login