Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta bukaci Sarakunan jihar su shirya addu’o’in zaman lafiya

Published

on

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bukaci dukkanin sarakuna, dagatai da masu unguwanni da su mayar da hankali wajen gudanar da addu’oin domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Gwamnan ‎ya bayyana hakan ne da yammacin jiya juma’a yayin wata ziyarar ta’aziyyar mahaifiyar Sarkin Rano Ambassador Muhammad Isa Umaru a garin na Rano wacce ta rasu makonni biyu da suka gabata.

Da yake nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umaru, ya bayyana matuƙar godiyarsa ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa jagorantar tawaga mai ƙarfi zuwa yi masa ta’aziyya.

Wakilin mu na gidan Gwamnatin kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa ‎Gwamna Abba ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan Hajiya maimuna, tare da sauran al’ummar musulmi baki daya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!