Connect with us

Labarai

Gwamnatin kano ta ce za ta magance matsalar zaizaiyar kasa a faɗin jihar

Published

on

Gwamnatin kano ta ce za ta tabbatar da magance duk wata matsalar Zaizayar ƙasa a dukkannin yankunan dake fama da matsalar a faɗin jihar, musamman a wannan lokacin na ƙaratowar damuna domin kare al’umma daga barazanar ambaliya.

 

Babban Sakataren a hukumar kula da sauyin yanayi da Zaizayar ƙasa na jihar kano Dakta Muhammad S Khalil ne ya bayyana hakan, ya ce gwamnati za ta  kawo karshen matsalar a wasu yankunan na jihar kano.

                   

Ya kuma ce nan bada jimawa bane gwamnatin za  tayi duk mai mai yuwuwa domin ganin ta shawo kan matsalar a cikin birni da kewaye musamman inda matsalar tafi kamari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!