Labarai
Gwamnatin Kano ta dage aikin tsaftar Muhalli na watan Yuli

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da dage aikin tsaftar muhallin da ta saba yi dukkan karshen wata.
Kwamishinan ma’aikatar Muhalli da sauyin Yanayi Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta Murtala Shehu Umar ya fitar.
Sanarwar ta ce, an dage aikin duben tsaftar ne saboda bikin yaye dalibai na jami’ar Northwest da za a yi a gobe Asabar.
Sanarwar ta ce, kwamishinan ya ce, yanzu haka za a gudanar da tsaftar muhallin a karshen watan Disamba mai kamawa.
You must be logged in to post a comment Login