Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Common entrance: Za a gudanar da tsaftar muhalli kamar kowanne wata – Dakta Kabiru Getso

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, za a gudanar da tsaftar muhalli na ƙarshen wata a gobe Asabar.

Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya tabbatar da hakan.

Cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar Sunusi Abdullahi Ƙofar Na’isa ta rawaito cewa za a yi tsaftar muhallin na duk gari kamar kowanne wata.

Sanarwar na zuwa ne yayin da ake ta yaɗa cewa an ɗage gudanar da duban tsaftar sakamakon jarrabawar da ɗaliban firamare za su yi a gobe Asabar.

A cewar Sanarwar jarrabawar kammala firamare ga ɗaliban ba za ta hana duban tsaftar muhalli ba.

A don haka ma’aikatar muhalli ta gargaɗi jama’a da su guje karya dokar hana fita daga ƙarfe 7 na safe zuwa 10 na safiyar Asabar ɗin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!