Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kano ta fara shirin raba kayan abinci ga talakawa

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, ta ce, za ta fara gudanar da abubuwan da za su samar da sauƙin matsalar yunwa da tsadar rayuwa da ake fama da su nan da kwanaki ƙadan masu zuwa.

Sakataren gwamnatin jihar Dakta Abdullahi Baffa Bichi, ne ya bayyana hakan a daren Asabar ɗin nan yayin da ya kai ziyara kanfanonin da gwamnatin ta bai wa aikin samar da shinkafa domin raba wa al’ummar jihar domin rage musu raɗaɗin janye tallafin man Fetur.

Dakta Abdullahi Baffa Bichi, ya kuma ce, a ƙalla kowanne kamfani zai samar da shinkafa sama da Tirela 30 na buhuna.

Haka kuma ya ce, gwamnatin Kano za ta samar da sama da Tirela ɗari na kayan abinci domin raba wa ga al’ummar jihar inda yanzu haka ake kan aikin tabbatar da hakan.

Rahoton: Umar Abdullahi Sheka

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!