Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta gargaɗi mutane kan karya dokokin tsaftar Muhalli

Published

on

Ma’aikatar Muhalli da sauyin yanayi ta Jihar Kano ta kai ziyarar duban tsaftar tashar mota ta Kano line A B wadda a yanzu ake kira KAROTA Motor Pack, inda ta bayyana takaicinta bisa yadda ta samu ɗaya daga cikin tashoshin cikin rashin tsafta.

 

Kwamishinan ma’aikatar Muhalli da sauyin yanayi Dakta Dahiru Muhammad Hashim ne bayyana hakan ta bakin Darakta mai Kula da gurbacewar Muhalli Malam Ibrahim Nasir Bunkure a safiyar yau yayin duban tsaftar tashar mota da kasuwni har ma da ma’aikatun gwannati.

 

Ibrahim Bunkure ya Kuma bai wa tashar wa’adin kwana biyu da su gyara kafin daukar matakin rufe tashar tare da cinsu tara

 

Muttaka Bala Sulaiman shi ne Shugaban tashar mota ta KAROTA Motor Pack, ya bayyana godiyarsa bi sa gyara da maikatar Muhalli ta musu inda ya ce zaiyi iya kokarin sa wajan ganin an gyara duk inda ya kamata

 

Ma’aikatar ta kuma yi  gargaɗi ga jama’a da su guji karya dokokin shirin tsaftar Muhalli na karshen wata-wata, domin gujewa daukar mataki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!